- Yan Najeriya da dama sun samu bashin gwamnatin tarayya na miliyoyin kudi domin rage radadi a lokacin annobar Corona
- Sai duk da bayyana yadda wadanda suka ci gajiyar shirin za su mayar da kudin, mutane da dama sun ki mayar da bashin kan lokaci
- Saboda haka gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar mayar da bashin cikin gaggawa ko kuma ta dauki wani mataki na daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Gwamnatin Najeriya ta fara barazana ga wadanda suka ci bashi a lokacin annobar Corona suka ki mayarwa.
A shekarar 2019 ne lokacin da annobar Corona ta ɓullo gwamnatin tarayya ta fara raba kudi domin rage matsin rayuwa.
'Aikin banza ake yi' Naziru Sarkin Waka ya ragargaji 'yan kirifto masu jiran ta fashe
Sai dai hukumar NASIMS ta wallafa a kafar Facebook cewa da yawa ba su mayar da bashin ba kuma gwamanti za ta dauki mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ku biya bashin Corona!" - NASIMS
A karon farko hukumar NASIMS ta fitar da sanarwa tana mai jan kunnen wadanda aka ba bashin da su gaggauta biya.
Ta ce hakan zai sa asusun bankunansu kubuta daga tsarin GSI na babban bankin kasa (CBN) wanda zai iya jawo kwashe kudi daga asusun ajiyarsu.
Corona: Matakin ƙarshe da za a dauka
Hukumar NASIMS ta bayya cewa an riga an ba bankuna umurni da su wawushe kudi a asusun duk wanda yaci bahsin yaƙi biya.
Za a rika wawushe kudin da ya shiga dukkan asusun bankin mutum har sai ranar da ya kammala biyan bashin da ya karba.
EFCC ta bankado badakalar kudi
Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta bayyana bankado wasu makudan kudi da ke da alaka da ayyukan jin kai a gwamnatin baya.
Rahotanni sun nuna cewa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari ne gwamnatin Najeriya ta yi ayyukan rabawa jama’a kudi da sunan tallafi.
Ana bincike kan tallafin Corona
A wani rahoton, kun ji cewa a shekarar 2023 majalisar wakilai ta ba wa AGF, Oluwatoyin Madein wa'adin sa'o'i 72 domin ta bayar bayani kan Naira biliyan 100 na tallafin COVID-19.
Kwamitin majalisar mai kula da asusun gwamnati ya zargi AGF da ƙin biyayya ga matsayar kwamitin na ta miƙa rahoto kan kuɗin a ranar 27 ga watan Oktoban shekarar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboN2hZJmnrCZnZa7tbWMrZhmnpGZtm7FwJ2bmmWqlnq1rYykrpqsn2Kvor%2FHoqVmnJFiwaJ50ZqZmmWRYrmwt8CcoKdlk6S%2FsLrAaA%3D%3D