- Yayin da tsoffin gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi ke cikin matsala, Aisha Yesufu ta yi musu shaguɓe a shafinta
- Aisha ta ce 'yan siyasar Najeriya sun dauka shekaru takwas wani abu ne inda ta gargade su kan amfani da lokacinsu
- Martanin na Aisha na zuwa ne yayin ake neman cafke Yahaya Bello da kuma kafa kwamitin binciken gwamnatin Nasir El-Rufai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Fitacciyar 'yar fafutuka a Najeriya, Aisha Yesufu ta yi shaguɓe ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da na Kogi, Yahaya Bello.
Aisha Yesufu ta yi hakan ne yayin da tsoffin gwamnonin ke cikin mawuyacin hali bayan kammala wa'adinsu a matsayin gwamnoni.
Wace shawara ta ba 'yan siyasar Najeriya?
Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan
Yesufu ta bayyana haka ne a shafinta na X inda ta ce 'yan siyasar Najeriya sun dauka shekaru takwas ba za su zo karshe ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ja kunnen 'yan siyasar Najeriya da su mayar da hankali yayin da suke kan madafun iko.
"A wurin 'yan siyasar Najeriya, shekaru takwas za su tabbata, abin da ba su sani ba kenan.""Ina dariyar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello."- Aisha Yesufu
Halin da El-Rufai da Bello ke ciki
Wannan martani na 'yar gwagwarmayar na zuwa ne yayin da tsoffin gwamnonin ke fuskantar matsaloli daban-daban.
A bangaren tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya na fuskantar zargin cin bashin miliyoyin daloli lokacin da ya ke mulkin jihar.
Kan haka ne, Majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin binciken bashi da kuma wasu badakalar kudi a gwamnatin.
El-Rufai ya shiga sabuwar matsala yayin da majalisar Kaduna ta kafa kwamitin bincike
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello na fuskantar zargin badakalar N84bn da hukumar EFCC ke tuhumarsa.
Hukumar ta yi wa gidan tsohon gwamnan kawanya a yunkurin cafke shi kan zargin badakalar kafin gwamna Usman Ododo ya tsere da shi.
Aisha ta magantu kan matakin Abba Kabir
A wani labarin, Aisha Yesufu ta yi martani kan matakin Abba Kabir na haramta fina-finan 'yan daudu.
Aisha ta ce tun kafin fitaccen ɗan daudu, Bobrisky ya waye ake ayyukan daudu a fadin jihar Kano.
Tsohon hadimin Muhammad Buhari, Bashir Ahmed ya caccaki Aisha inda ya yabawa gwamnan kan matakin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ5hJVwbGaZmai1onnYnqqunqViwaJ52KJkrKCRnMKmecaaZJ6kXafCp63IZpuaZamWtaLFwGaZnqScpHqsrc1mn5qkmaN6pa2MrKyknV2Ytqy1jK2YZpqRqMJuv8earpqqkWQ%3D